Rikicin kasar Rasha da Ukrani ya sa kasashen turai tsananin bukatar samar da makamashi daga kasar Iran, sai dai bai kamata a samu raguwar farashin danyen mai ba kafin Amurka ta biyawa Iran dukkan hakokinta da aka tabbatar mata ba.
Tawagar dake shiga tsakanin ta nuna cewa akwai bukatar Amurka ta biya diyya kan asarar rasa rayuka da ta jawo wa kasar Iran, kuma dole na cire takunkumin ya zama cikakke da zai yi tasiri kuma ya kare maslahar alumma. Kuma ya kasance a rubuce ba a fatar baki ba.
Daga karshe an bukaci Tawagar masu shiga tsakanin da ta su bukaci wadatattun lamuni na Tattalin arziki kimiyya da fasaha siyasa daga Amurka da kuma ba da tabbacin cewa Amurka ba za ta fice daga cikin yarjejeniyar ba bisa ka’ida ba kamar yadda tayi a baya.
342/